Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan yadda haramtaccen kasuwanci da cinikin kanana da manyan makamai suka mamaye nahiyar Afirka.

Shugaban ya kasashen duniya da su tashi tsaye wajen ganin sun shawo kan wadannan matsaloli domin hana tashe-tashen hankula da ayyukan ta’addancin da ake samu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yawan hare-haren ta’addancin da ake gani yau a duniya na tabbatar da wannan korafi da yake, musamman ganin yadda matsalar ayyukan ta’addanci suka addabi Najeriya, sakamakon rikicin Boko Haram da ‘yan bindiga da ke kai hare hare.

Ya ce wannan ya tilastawa kasar hadin kai da makotanta wajen yaki da ‘yan ta’adda musamman a Yankin Tafkin Chadi da kuma Sahel baki daya, yayin da yake jaddada matsayin gwamnatin tarayya na sake gina Yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *