Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yanke shawarar shiga yajin aiki na gama-gari daga ranar Litanin mai zuwa.

Daukar matakin ya biyo bayan wani taro da shugabanin ƙwadagon suka yi, mako guda bayan wa’adin makonni biyu da suka ba gwamnati na ta janye karin kudin man petur da wutar lantarki.

Tun dai a baya kungoyoyin sun ba gwamnatin tarraya wa’adin mako biyu domin janye ƙarin kuɗin man fetur da na lantarki da ta yi.

Mataimakin sakataren haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya, Kabiru Nasir ya ce akwai dalilai da dama da suka sa kungiyoyin suka yanke wannan shawarar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *