Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce za ta gudanar da taro gabannin zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kira domin nuna adawa da karin kudin man fetur da wutar lantarki.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai da hulda da jama’a Bello Barkindo ya fitar.

Sanarwar ta ce makasudin taron shine domin daidaitawa tare da cimma matsaya ta hanyar masalaha tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar kwadagon.

A cewar sanarwar akwai bukatar dukkanin gwamnonin jihohin Najeriya su halarci taron da zai gudana, saboda muhimmancin da yake dashi ga ‘yan Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa za a gudanar da taron ne yau Alhamis 24 ga watan Satumba da misalign karfe 6 na yamma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *