Gwamnatin tarayya ta ce ta amince da ƙudurin shimfiɗa layin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Katsina kuma ya dangana da jamhuriyar Nijar domin bunƙasa safarar kayayyaki.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai Garba Shehu ya bayyana haka, ya ce gwamnati za ta ciyo bashi don yin aikin, la’akari da cewa jirgin ƙasar zai mai da kuɗinsa nan gaba kadan.

Ya ce titin jirgin zai tashi daga Kano ya ratsa jihohin Katsina da Jigawa ya kuma kare a cikin Jamhuriyar Nijar.

Garba Shehu ya ce ana sa ran fara aikin ne a wata mai zuwa.

A cewar Garba Shehu samar da jirgin kasar zai zama babbar nasara ga Najeriya da Jamhuriyar Nijar ta fuskar kasuwanci, da inganta masana’antu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *