Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC Mai Mala Buni, da gwaman jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a fadarsa dake Abuja.

Duk da ba a bayyana abubuwan da shugabannin suka tattauna ba, wasu na ganin ganawar sirrin da suka yi bai rasa nasaba da sakamakon zaben gwamnan da ya gudana a jihar Edo.

Dan takaran jam’iyyar ta APC Osagie Ize-Iyamu, ya yi rashin nasara a zaben da ya kara da dan takaran jam’iyyar PDP wanda shine gwamnan jihar a halin yanzu Godwin Obaseki.

Ganduje wanda shine shugaban kwamitin yaki neman zaben gwamnan jam’iyyar a jihar, da takwaransa na jijhar Imo Hope Osodinma, sun yi kwanakin karshen mako a Benin saboda zaben.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *