Hukumar kayyade farashin man fetur ta Najeriya PPPRA ta ce gwamnatin tarayya ta kashe sama da naira trilliyan 8 a biyan tallafin man fetur daga shekarar 2006 zuwa 2015.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wasu bayanai da ta fitar a Abuja, ta ce an biya kudaden ne ga manyan dillalan man fetur da kuma kamfanin matatar man fetur na kasa NNPC. 

Sanarwar ta ce a shekarar 2006 kamfanin matatar man fetur na Najeriya ne babban sashen da ya fi karfi a aikin dakon man fetur daga kasashen ketare zuwa gida.

Hukumar ta ce a cikin sanarwar gaba da za ta fitar za ta bayyana yawan kudaden da aka fitar kafin sake fasalin wasu bangarori na man fetur.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *