Ma’aikatan lafiya a Najeriya sun janye yajin aikin da suka soma a tsakiyar watan Satumba kan bukatar inganta walwala, albashi da biyan su kuɗaɗen da suke bi na albashi.

Ƙungiyar ta ƙunshi ma’aikatan jinya da masu binciken jini da masu bayar da magani.

Babu dai wata hujja da ƙungiyar ta bayar kan janye yajin aiki duk da cewa ba a biya su bukatun su ba.

Sai dai ta ce nan gaba za ta sanar da sabon matakin da za ta dauka akan hakan.

Yajin aikin JOHESU ya soma ne kwana guda bayan ƙungiyar likitoci ta janye nata yajin aikin kan buƙatu iri guda.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *