Jami’an hukumar kiyaye aukuwar haddura 26 da aka yi garkuwa dasu a hanyar Mararraban Udege dake jihar Nasarawa sun kubuta daga hannun ‘yan ta’addan.

Gwamnan jihar Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Lafia.

Gwamnan ya ce jami’an hukumar 7 da aka kubutar a baya-bayan nan sune rukunin karshe da suka rage a hannun ‘yan ta’addan, da aka yi garkuwa dasu a makon da ya gabata.

A ranar 15 ga wannan watan ne jami’an tsaro suka kubutar da wasu 3 daga cikin mutanen, kwana guda bayan kubutar da wasu jami’an hukumar 10.

‘Yan ta’addan sun sace jami’an hukumar ne a lokacin da za su je wani shiri da hukumar ta shirya na samun karin hora kan makamar aiki a jihar ta Nasarawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bola Longe, ya tabbatar da haka a lokacin da yake magana a wani shiri na gidan radiyo da talabijin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *