Gwamnatin tarayya ta ce za ta cefanar da hukumar lura da harkokin fina-finai ta Najeriya domin ingantawa da kuma magance matsalolin da take fuskanta.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da kwamiti na musamman da zai yi aikin sauya fasalin hukumar.

Ya ce gwamnatin tarayya ta dauko kwararru da za su duba tare da bada shawarwari kan irin matakan da suka kamata a dauka domin kara inganta hukumar.

Muhammad ya ce hukumar da aka kafa domin kara inganta harkokin fina-finai, tare da samar da ci gaba, bata yi abin da ake bukata ba, kamar yadda aka tsara ta akai.

Ya ce tun bayan kafa hukumar, ta fuskanci matsaloli da dama, ciki harda gaza shirya wasu fina-finai da za su samar da kudaden shiga kamar yadda aka kafa ta akai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *