Kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin yaki da cutar korona, ya yi gargadi kan ci gaba da karya dokokin kariya daga kamuwa da cutar.

Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya bayyana haka a wajen taron manema labarai da kwamitin ke shiryawa a Abuja.

Ya ce ana ci gaba da samun saba dokokin kariya daga cutar, duk da cewa har yanzu Najeriya ba ta yi nasarar yakar cutar baki daya ba.

Mustapha ya kara da cewa takunkumin da ake sawa ana rufe baki da hanci saboda kariya an koma sa shi a kumatu, yayin da ake ci gaba da shirya tarukan jama’a ba tare da kula ba.

Ya kuma bukaci a ci gaba da yin taka-tsantsan domin gujewa sake bullar cutar da karfi kamar yadda ya faru a wasu kasashen turawa.

Ya ce gargadin ya zama wajibi, musamman kan yadda cutar ta yiwa tattalin arzikin Najeriya illa, idan aka kwatanta da yadda yake a shekarun da suka gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *