Karamin ministan ilimi na Najeriya Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce gwamnatin tarayya ta fara ba masu ruwa da tsaki horo na musamman kan sake bude makarantu domin ci gaba da karatu.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron kwana guda da aka shirya a Kano da masu ruwa da tsaki domin duba ka’idojin da suka kamata a abi wajen sake bude makarantun.

Nwajuba ya ce akwai shiri na musamman da ma’aikatar ilimi ta Najeriya ta yi domin fitar da ka’idoji tare da sanya ido kan yadda al’amura za su ci gaba da tafiya bayan bude makarantun.

A cewarsa shirin zai bukaci cikakken goyon baya daga masu ruwa da tsaki dan ganin an aiwatar dashi yadda ya kamata, tare da samun sakamako mai kyau.

Ya kara da cewa ganawar da masu ruwa da tsaki zai ba gwamnati damar sanin irin matakai da shawarwari da za ta yi amfani dasu dan samun nasarar da ake bukata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *