Babban alkalin kasar Kenya na son shugaba Uhuru Kenyatta ya rusa majalisar wakilan ƙasar saboda babu isassun mata kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Mai shari’a David Maraga ya ce majalisar ta gagara kawo daidaiton jinsi a cikinta.

Kundin tsarin mulkin Kenya ya tsara cewa wani jinsi ba zai mamaye sama da kashi biyu cikin uku na zaɓaɓɓu ko mukaman gwamnati ba.

A wata wasiƙa da ya aikewa shugaba Uhuru Kenyatta, babban mai shari’ar ya ce majalisar ta ka sa kiyayewa tare da amfani da sashen doka ta ya tabbatar da tsarin rabon kason maza da na mata a majalisa.

A cewarsa ƙin bin tsarin tamkar nuna wariya ne ga matan.

Sabuwar dokar da a ka aminta da ita a shekarar 2010, ta tanadi cewa kamata yayi a tabbatar da tsarin kashi biyu bisa uku na jinsi, to amma har zuwa yau maza ne ke ci gaba da mamaye majalisun dattawa da na wakilai a Kenya.

Sai dai shugaban majalisa Justin Muturi ya ce sam batun rushe majalisa ba abu ne mai yiwuwa ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *