Shugaban kasa Muhammdu Buhari, ya yi kira ga al’ummar jihar Kaduna su haɗa kai, su zama ‘yan’uwan juna domin sai an yi hakan sannan ci-gaba zai wanzu.

Buhari ya ce sai da zaman lafiya sannan a arziki da ci-gaban jama’a ke ɗorewa.

Ya ce Kashe-kashe da lalata dukiyoyi da kadarori ba ya haifar da komai sai zaman gaba da maida al’umma koma koma-baya.

Buhari ya yi kiran ne, a cikin jawabin sa na buɗe Taron Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar Kaduna karo na biyar.

Ya ce shirin ya yi nasara sosai, tun bayan fara taron a cikin shekara ta 2016, ya na mai cewa Jihar Kaduna ta cancanci jinjina, domin shekaru biyar kenan a jere duk shekara ba a fasa shirya taron ba.

Buhari ya ce Shirin ya kawo ci-gaba da bunƙasa Jihar Kaduna ta hanyar samun masu zuba jari da samar da ayyukan yi ga matasa da kuma kara samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnatin jihar.

“Nan na zo cikin 2017 na buɗe katafaren masana’antar abincin kaji da kuma wurin kiwon kajin a Olam Farm.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *