Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu babu wani tsayayyen lokacin bude makarantu a fadin kasar nan.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani jim kadan bayan fitowa daga taron masu ruwa da tsaki na shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya, karamin ministan Ilimi Chukwumeka Nwajiba ya ce bude makarantun ya na karkashin ikon jahohi.

Sai dai Chukwumeka ya ce dole sai sun samar da cikakken tsarin kariya daga cutar korana sannan za a bude makarantu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *