Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna, ya ayyana zaman makokin kwanaki uku domin alhinin mutuwar sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.

A cikin wata sanarwar da ya fitar, gwamnan ya ce a ranakun 21 da 22 ga watan Satumba za a sauke tuta, sannan a ranar 23 ga watan Satumba za ta kasance hutun aiki domin amfani da damar wajen taron addu’o’i ga sarkin.

Rahotanni sun ce, sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta makonni biyu a wani asibiti da ke Kaduna.

Sarkin dai ya kasance mafi ɗaɗewa a kan gadon sarauta a arewacin Nijeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *