Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya ce shugaba Muhammadu Buhari bai taba yin amfani da ikon sa ta fuskar da ba ta dace ba.

El-Rufai ya sanar da haka ne, yayin da yak e tsokaci a kan zaben gwamnan jihar Edo.

A yayin da yak e jawabi a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya ce ba kamar sauran gwamnatoci da su ka gabata ba, Buhari ya na bari a bar zabin jama’a a yayin zabe.

Ya ce da farko ya yi fatan samun nasara tare da sa rai har sai da makonni uku da su ka gabata, inda alamar faduwar su ta bayyana.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *