Gamayyar Ƙungiyar Dattawan arewa maso gabashin Nijeriya a kan zaman lafiya da ci-gaban al’umma, sun buƙaci shugaba Muhammadu Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron Nijeriya.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ta Zanna Goni, ta ce matsalar tsaro a Nijeriya ta na sake taɓarɓarewa.

Ya ce halin da ake ciki na bukatar sake sabon zubi a fanin hafsoshin da ke da ƙwarewa da sabbin shawarwari da dabaru a kan yadda za a fasalta sha’anin tsaro.

Sanarwar, ta ce yanayin tsaron Nijeriya a karkashin hafsoshin tsaro na yanzu ya kai mummunan yanayi, inda ƙasar nan baki ɗaya ta shiga damuwa saboda kashe-kashen farar hula da karuwar hare-hare da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Kngiyar, ta kuma bukaci shugaba Buhari ya saurari koke-koke da kiraye-kirayen ‘yan ƙasa na neman sake fasalta fanin tsaro.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *