Kwamitin shirya zaben gwamnan jihar Edo na jam’iyya APC, ya kalubalanci sakamakon zaben da hukumar Zabe ta bayyana, inda ta ce gwamnan jihar Godwin Obaseki da jam’iyyar PDP sun tafka magudi a zaben.

Haka kuma, Kwamitin a karkashin Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya ce an tafka magudi da aringizo a zabe da ya sa PDP ta yi nasara.

Sakamakon zaben da aka bayyana a garin Benin dai PDP ta samu Kuri’u dubu 307 da 955, yayin APC ta samu kuri’u dubu 223 da 619.

Kakakin kwamitin na jam’iyyar APC John Mayaki, ya ce jam’iyyar su ba ta yarda da sakamakon zaben ba domin an tafka magudi.

Ya ce Jami’an tsaro sun kama mutanen su babu gaira babu dalili, sannan an sauya alkaluman zabe a wasu wurare da dama ta hanyar kara wa dan takarar su kuri’un karya.

A karshe yayi kira ga magoya bayan jam’iyyar cewa su kwantar da hankalin su, jam’iyyar APC na duba yadda abubuwa su ka gudana a lokacin zaben, kuma nan da dan lokaci kadan za ta fitar da matsayin ta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *