Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin hamayarsa na Jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu.

Wannan ne karo na biyu da Obaseki ke doke Ize-Iyamu, inda a 2016 ma hakan ya faru, amma lokacin Obaseki na APC, Ize-Iyamu kuma a PDP.

Hukumar ta INEC ta bayyana cewa Obaseki ya samu ƙuri’u 307, 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 223,619.

Ɗan takarar Jam’iyyar SDP ne ya zo na uku da ƙuri’u 323, sai kuma na Jam’iyyar LP da ya samu ƙuri’u 267.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *