Dakarun Sojin Najeriya na rundunar Operation Thunder Strike sun dirar wa ‘yan bindiga tare da tarwatsa sansanin su a dajin Kuyambana da ke Jihar Kaduna.

Daraktan samar da bayanai na rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar a nan Abuja.

Ya ce sojojin sun dandana wa ‘yan bindigar kudar su da jerin hare-haren da suka kai a dajin na Kuyambana.Manjo Janar Enenche, ya ce an kai hare-haren ne bayan samun muhimman bayanai da suka kai ga gano maboyar ‘yan ta’addan da kuma wurin da suke taro.

Ya kara da cewa sun kuma yi amfani da jiragen rundunar sojin saman Najeriya wajen kai wasu daga cikin hare-haren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *