Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya koka da yadda mayakan Boko haram ke jan ra’ayin kananan yara sakamakon fatara da rashin ayyukan yi a jihar.

Gwamnan ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya ke bayyana kalubalen da ake fuskanta a sansanin ’yan gudun hijira, bayan ya karbi bakuncin wasu ’yan majalisar wakilai da suka kai masa ziyara a Maiduguri.

Zulum, ya ce, akwai sama da manoma ’yan gudun hijira dubu 700, a Monguno da kuma fiye da dubu 400, a Gamboru Ngala da ba su iya zuwa noma gonakin su.

Ya ce, zaman dirshan da manoman majiya karfi ke yi a sansanin ’yan gudun hijira ka iya kawo rashin tsaro wanda zai sa matsalolin da ake fuskanta a yanzu su ta’azzara.

Gwamna ya ce mafita a nan kawai ita ce a san yadda za a bi a mayar da wadannan mutanen garuruwan su cikin gata, amma idan ba haka ba, za a iya fuskantar babbar matsalar da ta fi wadda ake ciki a yanzu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *