Gwamnatin jihar ta ce ta na shirin fara aiwatar da wani sabon tsarin da zai taimaka wajen yaki da matsalar ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu sassan jihar.

Shugaban kwamitin tsaro na jihar Dr. Mustapha Inuwa, yace daukar matakin zai dakile duk wata mafakar wadanda ke amfani da hanyar su na shiga garuruwan Babban Duhu, da Lamma, da Kurfi da sauran su.

Mustapha Inuwa, ya ce an yake shawarar cewa, za a maida dajin ya zama gonaki, kuma wadanda ke sha’awar a yanka masu su yi gidaje a wurin za su samu dama, yayin da ya ce tuni gwamnati ta bada umurnin a fara aikin kawar da manyan itatuwa.

Wata majiya ta ce, za a maida dazuzzukan da maharan ke boyewa su zama filaye da gonakin noma ne ga maharan da su ka tuba da sauran jamar da su ka nuna sha’awar su.

Mustapha Inuwa, ya kara da cewa har yanzu kofar yafiya ga maharan a bude ta ke, illa dai tsarin ya koma hannun sojojin Nijeriya ne.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *