Gwamnatin jihar Kogi ta aike wasikar martani ga gwamnatin kasar Amurka dangane da haramta wa gwamnan jihar Yahaya Bello shiga kasar ta, sakamakon zargin cewa ya yi magudi a zaben gwamnan jihar day a gudana a watan Nuwamban 2019.

A cikin wasikar, gwamnatin ta ce kamata ya yi Amurka ta ba gwamnan damar kare kan sa.

Wani sashen wasikar da sakatariyar gwamnatin jihar Folashade Arike Ayoade, ta aike, ya ce ba za su amince da hakan ba, domin idan da gaske su na yi ne don gyaran demokradiyya akalla ya kamata su ji daga bangarorin biyu.

Gwamnatin, ta ce duk da cewa an samu kalubale daban-daban a zaben gwamnan da aka yi bara, za a yi gyara a zabubbuka masu zuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *