Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kirkiro sabuwar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar sarrafa kayayyakin da kudaden almundahana da aka kwato.

Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa dake Abuja.

Malami ya ce majalisar ta amince da turawa majalisun dokoki sabuwar dokar kafa hukumar domin neman amincewarsu kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Malami, ya ce da zarar an amince da kafa hukumar, za ta maida hankali kan sanya ido da kuma taimakawa wajen gudanar da kadarorin da kudaden da aka kwato daga hannun masu almundahana.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *