Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda da dama a maboyarsu dake dajin Kwiambana a jihar Zamfara.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na shelkwatar tsaro Majo Janar John Enenche ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce rundunar sojin ta kai harin ne ta sama da kuma jirgin yaki na runduna ta musamman da ke yaki da ayyukan ta’addanci da ake yiwa lakabi da Operation Hadarin Daji.

Sanarwar ta ce rundunar ta ce baya ga kashe ‘yan ta’addan harin ya lalata maboyarsu da kuma sauran sansanoninsu da suke amfani dashi wajen shirya kai hare-hare.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *