Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya ce ya zama wajibi a dauki matakan farfado da tattalin arziki na cikin gida domin shawo kan tafiyar hawainiya da ake samu na ci gaba sakamakon bullar cutar korona.

Mai taimakawa shugaban majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Ezrel Tabiowo, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a wajen taro na musamman da aka shirya domin kara fito da muhimmancin amfani da kayayyakin da aka samar a cikin gida.

Kwamitin kula da kayayyakin da aka samar a cikin gida na majalisar tare da hadin gwiwar kwamitin majalisar wakilai ne suka shirya taron, domin fito da muhimmancin da hakan ke da shi wajen bukasa tattalin arzikin kasa.

Lawan ya ce taron wanda shine irinsa na farko da ya tattaro bayanan masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen fito da shawarwari na matakan da suka kamata a dauka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *