Kungiyar kwadago ta Najeriya ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 ta janye matakin karin kudin man fetur da wutar lantarki ko ta tsunduma yajin aiki.

Shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin gudanarwa a Abuja.

Ya ce ma’aikata da kuma sauran ‘yan Najeriya basa farin ciki da matakin da gwamnati ta dauka na kara kudaden farashin.

Shugaban ya ce kungiyar na mamakin yadda a daidai lokacin da sauran kasashe ke saukakawa al’ummominsu, tare da basu tallafi, gwamnatin tarayya ke kara daukar irin wadannan tsauraran matakai.

Wabba ya kara da cewa kwamitin ya gana tare da maida hankali ne kan irin wahalhalu da annobar korona ta jefa ‘yan Najeriya a ciki, kuma zai hada kawunan bangarori da dama tare da nuna rashin amincewarsu da tsarin da ya sake jefa da dama daga cikin ‘yan Najeriya a talauci. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *