An kama mutane 7 cikin fursunoni 219 da suka tsere daga wani gidan yari a garin Moroto da ke arewa maso yammacin Uganda.

An bayyana cewa fursunonin sun gudu da bindigogi 15 da harsasai masu yawa.

Fursunonin sun harbe wani soja wanda ya yi yunƙurin tare su.

Jami’an gidan yari da kuma sojojin ƙasar sun ƙaddamar da wani shiri na musamman domin gano su, yayinda ake kyautata zaton sun tsere zuwa kan iyakar ƙasar da Kenya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *