Gwamnatin tarayya ta sha alwashin tabbatar da an kwatowa ‘yan kasuwar Najeriya dake harkokinsu a kasar Ghana ‘yan ci kan abubuwan da suka faru dasu.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya tabbatar da haka a lokacin da yake magana a taron wakilan ‘yan Najeriya dake zaune a kasar ta Ghana.  

Taron wanda ya gudana a gidan jakadan Najeriya dake Accra a birnin Ghana, ya maida hankali kan matsalolin da ‘yan kasuwar ke fuskanta, da suka hada da rufe shagunansu.

Mataimakin shugaban kasan ya ce ya bibiyi dukkanin abubuwan dake faruwa a kasar ta Ghana, kuma gwamnatin tarayya na daukar matakan da suka kamata.

Tunda farko mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya Kozito Obiorah, ya gabatarwa mataimakin shugaban kasar takardun korafe-korafe akan batun.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *