Gwamnatin Tarayya ta yi ikirarin cewa, tsananin tausayin ‘yan Nijeriya ne ya sa aka kara farashin man fetur zuwa naira 161, amma naira 181 ya kamata a ce ana saida shi.

Karamin Ministan man Fetur, Timipre Sylva ya bayyana haka, yayin ganawa da tawagar gwamnatin tarayya da shugabannin Kungiyar Kwadago ta Kasa da aka yi a Abuja.

Gamayyar Kungiyar Kwadago ta Kasa dai ta nemi gwamnati ta janye karin kudin man fetur, ko kuma a shiga yajin-aikin da zai tsaida harkokin gwamnati gaba daya.

Da yak e bayyana wa Kungiyar Kwadago dalilan karin kudin man, Sylva ya ce gwamnatin tarayya ba ta iya jure biyan manyan dillalan da ke shigo da fetur kudin tallafin mai, don haka ne aka kara kudin fetur saboda an daina biyan kudaden tallafin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *