A ci-gaba da neman madadin man fetur a fannin tattalin arzikin Nijeriya, shugaban Hukumar Kula da Tasoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Alhaji Hassan Bello, ya ce kudin fito na iya maye gurbin abin da mai ke samarwa.

Ya ce dogaro da Man fetur na maida tattalin arzikin Nijeriya baya, kuma duk kasar da ta kasance ba ta da ingantaccen tsarin sufurin jiragen ruwa za ta samu nakasun tattalin arziki.

Hassan Bello, ya ce hukumar shi ta dukufa wajen ganin an samu tsari mai nagarta a bangaren shige da ficen jiragen ruwa, wanda yanzu haka su ka kammala duk wasu shirye-shirye don ganin an saukaka wa ‘yan kasuwa hanyar shigowa da fitar da kayan su a Nijeriya.

Ya ce nan da farkon shekara ta 2021 za su share wa ‘yan Nijeriya hawaye, ta yadda za su rika cika takardun neman izinin shiga ko fitar da kayan su ta kafar yanar gizo, sannan su na aiki tukuru domin rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa, musamman a birnin Ikko.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *