Majalisar wakilai na yunkurin tilasta wa shugaban kasa aiki da tsarin raba dai-dai wajen nada mukaman manyan hafsoshin sojin Nijeriya.

Yunkuri dai ya zo ne a cikin wani sabon kudiri da ya ke kokarin yi wa dokokin shekara ta 2019 na gidan soji garambawul.

 Dan majalisa Awaji-Inombek Abiante, ya ce ya lura babu adalci a rabon mukaman tsaro a gwamnatin tarayya, don haka ya nemi a tilasta wa shugaban kasa ya yi la’akari da dukkan bangarori. 

 Da ya ke hira da ‘yan jarida a game da kudirin, Abiante ya ce nadin da shugaban kasa ya yi ya janyo rabuwar kan ‘yan kasa, domin shugaban hafsan tsaro Janar Gabriel Olonisakin ya fito ne daga Kudu maso yamma, sai kuma Janar Tukur Buratai da ya fito daga Arewa maso gabas.

Sai kuma mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Janar Babagana Monguno da ya fito daga Arewa maso gabas, da kuma shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya da shugaban shugaban hukumar tsaro ta DSS daga Arewa maso yamma da tsakiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *