Majalisar dattawa ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a fadin Nijeriya cewa, kada su kashe tattalin arzikin kasar nan ta hanyar daukar salon Turawa wajen yaki da annobar korona.

Sanatocin sun tattauna ne da kwamitin jiragen sama da lafiya na majalisar dattawa da masu ruwa da tsaki a kan yadda cutar korona ta kara kamari a Nijeriya da sauran kasashen Afrika.

Shugaban kwamitin Sanata Smart Adeyemi, ya ce duba da yadda cutar ta ke, ba daidai ba ne a ce Nijeriya ta na kwaso tsarin yakar cutar daga kasashen Turai da Amurka ko kuma China.

Sai dai shugaban kwamitin yaki da annobar na fadar shugaban kasa  Dr. Sani ALiyu ya tabbatar da cewa, talauci ya na daya daga cikin manyan makaman da su ka yaki cutar korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *