Gwamnatin Burtaniya ta yi barazanar sanya haramcin shiga kasar ta a kan duk wani ɗan Nijeriya da aka samu da hannu a rikicin zaɓe gabanin zaɓubbukan gwamnan da za a yi a karshen wata.

Birtaniya, ta kuma yi barazanar karbe kadarorin ketare na duk wani ɗan siyasa da aka samu da laifi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Burtaniya ta ce za ta tura masu sa ido a zaɓubbukan gwamnan jihohin Edo da Ondo.

Jakadan Burtaniya a Nijeriya ya tattauna da shugabannin manyan ‘yan siyasar Nijeriya biyu domin jan hankalin su da bukatar zaɓe cikin kwanciyar hankali.

A ranar 19 ga watan Satumba ne za a gudanar da zaɓen jihar Edo, yayin da za a gudanar da na jihar Ondo a ranar 10 ga watan Oktoba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *