Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa NEMA, ta fara rabon hatsi Ton dubu 3 da 659 ga gidaje dubu 80 da 405 a jihar Sokoto, a wani mataki na tallafa wa mutane sakamakon matsin da su ka shiga yayin kullen annobar korona.

Shugaban hukumar Muhammadu Muhammed ya bayyana haka, yayin da ya ke mika wa gwamnatin jihar Sokoto kayan abincin a gidan gwamnati.

Muhammed, wanda ya samu wakilcin Dr Onimode Bandele, ya ce gwamnatin tarayya ta samar da hatsin da za a raba wa mutane masu karamin karfi a jihar domin rage radadin kullen korona da aka sa domin dakile yaduwar annobar.

Ya ce an bada hatsin ne domin a raba a matsayin tallafi ga marasa karfi da kullen cutar korona ya shafa.

A jawabin sa, gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jinjina wa gwamnati bisa tallafin, inda ya ce zai taimaka sosai wajen rage wa mutane wahalhalun da su ke ciki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *