Hukumar kiyaye aukuwan haddura ta Najeriya FRSC ta tabbatar da cewa wasu ‘yan ta’adda sun kashe jami’anta biyu a Mararraban Udege dake jihar Nasarawa.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Bisi Kazeem, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce baya ga mutanen da aka kashe, ‘yan ta’addan sun kuma yi garkuwa da wasu karin 10.

Kazeem ya ce ‘yan ta’addan sun kaiwa tawagar hukumar ta mutane 26 hari ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta tafiya daga Sokoto zuwa Kebbi, domin samun wani horo na musamman.

Sanarwar ta ce tuni Shugaban rundunar Boboye Oyeyemi, ya sanar da hukumomin da abin ya shafa domin fara gudanar da aikin ceto, tare da gudanar da binciken da ya kamata.

Sannan ya bukaci sauran jami’an hukumar da kada su karaya sakamakon faruwar wannan lamari, yana mai cewa za su ci gaba da aiki da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da an hukunta masu hannu a irin wadannan ayyukan ta’addanci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *