Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya ce rundunarsa ta tura da akalla jami’an tsaro dubu 31 jihar Edo gabannin zaben gwamna da za a gudanar a jihar.

Adamu ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki, da hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya a Benin. 

Ya ce rundunar ba ta da wata fargaba akan barazanar tashin hankali dake dabaibaye da yakin neman zaben da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Adamu ya kara da cewa a shirye rundunar take wajen tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma, tare da samar da yanayi mai kyau ga masu kada kuri’a.

Ya ce taron da aka gudanar da masu ruwa da tsakin wanda ya kunshi wasu daga cikin ‘yan takaran zai taimaka wajen shawo kan duk wata baraka da aka iya tasowa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *