Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta bukaci gwamnatin jihar Plateau ta dauki matakan kariya domin dakile matsalar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar.

Shugaban hukumar na kasa Muhammad Mohammed, ya bukaci hakan  a lokacin da ya kai ziyara da gwamnatin jihar da kuma sansanin rundunar soji dake jihar.

Mohammed wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban sashen kula da harkokin kudi na hukumar Sani Jibba, ya ce jihar na daya daga cikin jihohi da ake fargabar samun ambaliya a Najeriya.

Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa ana iya samun ambaliyar ruwan ne a kananan hukumomin Barikin Ladi, Pankshin, Jos ta kudu, Jos ta Arewa, Kanke, da kuma Mangu.

Ya ce babban abin da ya kamata gwamnatin jihar ta yi shine ta umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jiha, tayi aiki da kananan hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakan da suka kamata.

Sannan ya bada tabbacin cewa bisa ga goyon bayan duka bangarori, hukumomin za su ji saukin daukar matakan gaggawa da zarar iftila’in ya auku.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *