Hukumar yaki da masu fataucin bil’adama ta Najeriya ta ce za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana dan ganin an maido da mutanen da aka yi fataucinsu.

Shugabar hukumar Julie Okah-Donli, ya bayyana haka a wajen wani taro na musamman da aka shirya domin maido da mutanen da aka yi fataucinsu gida.

Ta ce kare ‘yancin wadanda aka yi fataucinsu na da matukar muhimmanci, kuma hukumomin za su ci gaba da maida hanakali akan hakan.

A cewarta sanin kowane kasashe ba sa mutunta mutanen da aka yi safararsu, domin ana musu kallon wadanda suka saba dokokin kasashen duniya.

Ta kara da cewa a shekarar 2018, gwamnatin tarayya ta fito da wani shiri na musamman domin maido da mutanen da aka yi safararsu ba bisa ka’ida ba, wanda daga bisani aka basu horo na musamman tare da wayar musu da kawuna ta yadda za a dakile faruwar haka a nan gaba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *