Gwamnatin tarayya ta ce daga watan Oktoba mai zuwa za ta fara maida motoci da injinan samar da wutar lantarki su rika amfani da iskar gas maimakon man fetur.

Karamin ministan man fetur Timipre Sylva, ya bayyana haka a lokacin da ake hira da shi a cikin wani shiri na gidan talabijin na kasa, kan karin kudin man fetur.

Sylva ya ce gwamnatin tarayya za ta dau wannan matakin ne domin saukakawa ‘yan Najeriya tsadar man fetur da suk fuskanta bayan cire tallafin man.

A cewarsa motoci da sauran ababen hawa na iya amfani da man fetur ko kuma iskar gas a kowani lokaci.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta yi hakan a wani shiri da ta fito dashi a garin Port Harcourt dake jihar Rivers, inda ta maida mashina masu kafa uku zuwa amfani da iskar gas, kuma anyi nasara a shirin.

Ya kara da cewa za a fada shirin zuwa kananan injinan samar da wutar lantarki da ake amfani dasu a gidaje.

A cewar tsohon gwamnan na jihar Bayelsa, gidajen mai mallakin matatar man fetur na kasa NNPC ne za su fara saidawa ababen hawa iskar gas din.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *