Kasar Amurka ta sanya haramcin bisa kan wasu ƴan siyasar Najeriya da ake zargi da yiwa harkokin zaɓe zagon-kasa a zaɓukan gwamnan jihohin Edo da Ondo.

Haka zalika haramcin ya shafin ɗaiɗaikun mutane da ta zargi cewa sun yi katsalanda a zaɓen watan Nuwamba 2019 na gwamnan Kogi da Bayelsa.

Sanarwar da jami’in yada labarai na ma’aikatar harkokin wajen Amurkan, Morgan Ortagus ta fitar, ta ce mutanen da aka sanyawa wannan takunkumi na yiwa harkokin demokradiyar Najeriya zagon-kasa.

Morgan ta kuma bukaci hukumar zaɓe, ƴan siyasa da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen Edo da Ondo su kwatanta adalci da mutunta demokradiya.

Sai dai kasar ba ta bayyana sunayen mutanen da aka sanyawa wannan takunkumi ba, da kuma yadda gwamnati ta zabo sunayen mutanen.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *