Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Mahmood Yakubu, ya ce za a hukunta duk mutanen da aka samu suna saba dokokin zabe a zaben gwamnan jihar Edo da zai gudana ranar Asabar mai zuwa.

Yakubu, ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya gabannin zaben a Benin.

Ya ce sayen kuri’un jama’a, satar akwatunan zabe, aringizon kuri’u karkatar da kayayyakin zabe da sauran su na daga cikin manyan laifukkan da hukumar ta hana.

Yakubu ya ce shelkwatar hukumar za ta sanya ido akan harkokin zaben ta fasahar zamani, domin tabbatar da cewa ba a samu matsaloli ba.

Sannan ya ba ‘yan jihar ta Edo tabbacin kuri’unsu za su yi tasiri akan zabo wanda zai zama gwamnan jihar, adon haka su maida hankali wajen cin romon demokradiyya.

Ya ce hukumar za ta samar da wasu na’urori na suka hada da gilasan ido, da sauran su, domin saukakawa masu bukata ta musamman dake son kada kuri’a.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *