Kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar korona ta ce Najeriya na samun nasara a matakan da take dauka na yaki da cutar a fadin kasar nan.

Shugaban hukumar wanda shine sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana haka a lokacin da yake magana a wajen taron da kwamitin ke shiryawa a Abuja.

Ya ce ana ci gaba da samun raguwa masu kamuwa da cutar a kullum, yayin da ake ci gaba da gudanar da gwaje-gwajen mutane a jihohin dake fadin kasar nan.

Ya ce matakan da ake dauka wajen yaki da cutar ya taimaka wajen raguwar masu kamuwa da cutar, duk da cewa ba hakan yake nuna cewa an yaki cutar baki daya ba.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan matakin da kungiyar likitoci ta Najeriya ta dauka na shiga yajin aiki, a cewarsa ma’aikatan lafiya na bada gaggarumar gudunmawa wajen dakile yaduwar cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *