Gwamnatin jihar Kaduna ta ce nan gaba kadan za ta fara fitar da Naira milliyan dari biyu domin tallafawa mata a fadin jihar.

Kwamishinan kula da harkokin mata da ci gaba ta jihar, Hafsat Baba ta sanar da haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a Kaduna. 

Kwamishinar ta ce an samar da kudaden ne karkashin shirin horar da mata kan sana’o’i domin bunkasa kananan da matsakaitan sana’o’i a tsakanin mata a jihar.

A cewarta an kafa wani kwamiti na musamman da zai biyiyi shirin da aka gudanar a kashi na farko, tare da bada shawarwari akan irin matakan da za a dauka a kashi na biyu. 

Ta kara da cewa matan za su iya samun tallafin naira milliyan 2 ta hanyar amfani da kungiyoyin da suka kafa.

A kan batun biyan bashi kuwa, Hafsat ta ce gwamnatin tarayya ta umurci babban bankin Najeriya CBN ya rike asusun ajiyar banki na wadanda suka ci bashi suka ki biya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *