Kungiyar Yarabawa mazauna jihar Kogi, sun ce su na da bukatar tattara komatsan su su bar yankin Arewa bayan shafe tsawon shekaru su na rayuwa a ciki.

Yarbawan sun ce, a baya sun zabi barin ‘yan’uwan su da mahaifar su a jihohin Ondo da Ekiti da Kwara saboda dogaro da kai, yanzu kuma akwai bukatar su koma cikin dangin su.

Sun bayyana haka ne a karkashin kungiyar su mai suna OLA a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, inda shugaban kungiyar Chief Emmanuel Otitoju ya ce sun aika wa majalisar dokoki ta tarayya sakon bukatar su.

A cewar sa, tuni kungiyar su ke da kundin tsare-tsaren da majalisar dokoki ta tarayya ta sanya wa hannu, a yanzu kuma su ke son a sabunta dokar domin kare ‘yancin ire-iren kungiyoyin su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *