A wani harin da ‘yan bindiga su ka kai Garin Udawa da ke Karamar Hukumar Chukun ta Jihar Kaduna, sun yi awon gaba da mutane 17, bayan sun kama wata maijego da jaririn da ta ke shayarwa.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata, yayin da mutanen ke kan hanyar su ta zuwa gona kusa da Gonar Lema, kuma duk wadanda aka yi garkuwar da su ‘yan gida daya ne.

Wata majiya ta ce , Kafin ‘yan bindigar su samu nasarar arcewa da mutanen, sai da su ka kashe mutum daya sannan su ka raunata mutane hudu.

Mai Unguwar yankin Yakubu Hussaini, ya ce wadanda aka yi wa raunin duk ‘ya’yan Yakubu Gurmi ne, wanda yanzu haka ya na kwance a Asibitin Birnin Gwari ya na jiyyar harbin da aka yi ma shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *