An samu dan yamutsi bayan shugaban kwamitin binciken Magu Ayo Salami ya umarci wasu lauyoyin Magu su fice daga dakin da kwamitin ke zaman a fadar shugaban kasa.

Ayo Salami dai  shi ne shugaban kwamitin bincike da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa domin bankado cin hanci da kwato kadarorin gwamnati.

Mai shari’a Salami, ya umarci jami’an tsaro su fitar da wasu lauyoyin Ibrahim Magu guda biyu, wadanda su ka hada da wata Zainab Abiola da Aliyu Lemu jim kadan bayan gabatar da su.

An dai fara samun matsala ne bayan shugaban tawagar lauyoyin Magu Wahab Shitu ya mike domin gabatar da sauran abokan aikin sa.

Sai dai Salami ya katse ma shi hanzari, ta hanyar sanar da shi cewa shi kadai za a bari ya kare Ibrahim Magu, inda bayan nan ne ya umarci jami’an tsaro su fitar da sauran lauyoyin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *