Ministan yada Labarai Lai Mohammed ya tada kura a shafukan sada zumunta, sakamakon sanarwar da ya fitar cewa in da a ce  Buhari bai zama shugaban kasa ba da tuni Nijeriya ta durkushe.

Wata Sanarwa da ofishin Ministan ya fitar, ta ce zaman Buhari shugaban kasa a shekara ta 2015 ne ya hana Nijeriya durkushewa bayan an shafe tsawon lokaci ana shugabanci maras alkibla.

Ministan ya ce, Shugaba Buhari ya karbi jagorancin Nijeriya ne yayin da aka mamaye yankuna da dama, lokacin da garuruwa da birane da dama ciki har da Abuja su ka zama filin wasa ga ‘yan ta’adda kuma a lokacin aka sace arzikin Nijeriya.

Sai dai tun daga lokacin da aka fitar da wannan sanarwa, ‘yan kasar musamman a shafin sada zumunta na Twitter su ke bayyana ra’ayoyin su, inda galibi su ke sukar ministan a kan kare gwamnati duk da abin da su ka kira gazawar gwamnatin Shugaba Buhari.

Wani mai amfani da shafin Twitter, Daniel Tawire, ya ce Lai Mohammed zai kare gwamnatin su ko da yaushe duk da cewa ta gaza saboda ya na cikin wadanda su ka gaza, yayin da wasu ke ganin kalaman ministan wata hikima ce ta janye hankalin ‘yan Nijeriya daga tunanin mawuyacin halin da su ke ciki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *