Gwamnatin Tarayya ta bayyana yajin aikin da gamayyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta JOHESU ta fara a matsayin karya doka.

Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi Chris Ngige ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da mataimakin kakakin Ma’aikatar Ƙwadago ta Nijeriya ya fita.

Ngige, ya ce Gwamnatin Tarayya ta umarci ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin JOHESU su dakatar da yajin aikin.

Ministan, ya kuma shawarci ƙungiyoyin su sake tunani game da yajin aikin, wanda ba ya kan ƙa’ida ta hanyar fifita mahimmancin lafiyar mutane fiye da komai.

JOHESU dai ta ɗauki matakin ne, bayan kwamitin gudanarwar ta na ƙasa ya yi wata ganawa a ranar Asabar da ta gabata, inda ta ce ta fara yajin aikin bayan ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 15 domin a biya mata buƙatun ta, amma babu abin da aka yi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *