A shirin tantance ma’aikatan kananan hukumomi 27 da gwamnatin jihar Borno ke yi, ta ce ta samu rarar sama da Naira miliyan 150 da ake biyan wasu ma’aikatan bogi fiye da dubu tara a kananan hukumomi 19.

Gwamnatin jihar Borno ta gudanar da aikin tantance tsarin biyan ma’aikatan ne a cikin wata guda, ta kuma gano wasu ma’aikata masu karancin shekaru da wadanda shekarun su ya haura na aiki a kananan hukumomi 19.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, ya ce an samu rarar sama da aira miliyan 57 tsakanin ma’aikatan da shekarun su ya haura 60, sannan samu rarar sama da Naira miliyan 93 tsakanin wasu da su ka karbi takardun tantancewa amma basu bayyana a gaban kwamitin ba, wanda hakan ke tabbatar da dukkan su ma’aikatan bogi ne.

Shugaban Ma’aikatan kananan hukumomi Mustpha Bulama, ya ce su ma ma’aikatan ba su da ra’ayin a kyale mutanen da shekarun su ya kai 60 su cigaba da aiki saboda yaran da ke tasowa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *